Wata kungiyar matasa a Arewa-maso-Gabas Youth Transformation Forum, ta caccaki shirin gwamnatin tarayya na haramta goyo a babura kasuwanci da aka fi sani da ‘Achaba’.

Ƙungiyar ta soki yunkurin gwamnatin na duba yiwuwar hana goyo a babura a dukkanin faɗin kasar.

Yayin da Achaba ke da fa’ida, masu aikata laifuka suma suna amfani da shi wajen aikata munanan laifuka a wasu sassan ƙasar.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta yi tunanin hana baburan kasuwanci a fadin kasar nan a wani mataki na magance matsalolin tsaro.

Sai dai kungiyar ta bakin shugabanta, Comrade Abdulrazak Albani, ta yi Alla-wadai da matakin, inda ta jaddada cewa ‘yan Najeriya kimanin miliyan 98 sa su shiga mawuyacin hali.

A cewarsa, a cikin mutane miliyan 200 da ke kasar, sama da miliyan 98 na al’ummarta na fama da matsanancin talauci kuma ba su da motocin da za su bi, hana achaba zai kara sanya masu rauni da zullumi.

Albani ya bayyana cewa baya ga yin wahalar sufuri ga talakawa ‘yan kasa, matakin zai sa masu tuka babura su rasa aikin yi tare da kara yawaitar laifuka a cikin al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: