Jami’ar Crown University International ta karrama Falakin Shinkafi Ambasada Dakta Yunusa Yusuf Hamza da lambar karrama ta Dakta (Dr.)

Sanarwar karramawar na nabcikin wata wasika mai kwanan watan 07 ga watan Yunin shekara ta 2023, kuma ta na sanye da sa hannun Magatakardar jami’ar Farfesa Sir Abhiram kukshicshka.
A cikin wasikar an bayyana cewa dukkanin masu ruwa da tsaki a jami’ar sun amince da karramawar bisa cancantarsa.

Kuma karramawar ta samu sahalewa daga dukkan hukumomi masu lura da irin wannan lambar yabo na kasar Amuruka.

Jami’ar Crown University International wadda ke da reshe a Nigeria, ta karrama Falakin Shinkafi ne sakamakon wasu abubuwa da tayi la’akari da shi waɗanda suka hadar da taimakawa Masu Karamin karfi don ganin sun sami nagartacce Ilimi domin cigaban al’umma.
Ambasada. Dakta Yunusa (Falaƙin Shinkafi) ya samu lambar yabo daban-daban bisa ayyukan jin kai da ya ke yi a cikin al’umma.