Gwamnati Jihar Bauchi ta bayar da umarnin daukar sabbin Likitoci 252 a Jihar.

Mai magana da yawun shugaban ma’aikatan Jihar Umar Sa’idu shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ya aike wa manema Labarai a jiya Juma’a.

Umar Sa’id ya ce wannan na daga cikin manufofin gwamnatin Jihar na samar da ayyukan yi ga matasan tare da bunkasa harkar lafiya a Jihar.

Shugaban ma’aikatan Jihar Alhaji Yahuza Adamu Haruna ya ce tuni Ofishin sa ya kammala duk wani shiri na daukar daliban da su ka karanci fannin aikin Lafiya.

Alhaji Yahuza ya kara da cewa gwamnatin na kokari matuka wajen ganin ta tabbatar da dorarriyar lafiyar Al’ummar ta a fadin Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: