Connect with us

Labarai

Hukumar EFCC Ta Aike Da Jami’anta Kasuwar Chanjin Dala Da Ke Abuja Domin Kama Masu Boye Dalar

Published

on

Jami’an Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC sun yi dirar mikiya a kasuwar chanji ta Zone 4 a birnin tarayya Abuja domin kama wadanda su ka boye dala.

Jami’an su kai sumamen ne sakamakon wasu “yan kasuwar da su ke boye dalar Amuruka wanda hakan ke sanyawa farashin kayayyaki ya ke tashi a Najeriya.

Jami’an sun ce yin hakan da “yan kasuwar su ka yi ya haddasa faduwar naira a kwanakinna.

Ba tun yanzu ba jami’an sun dade su na sanya idanu akan yan kasuwar ta chanji dala wanda su ke boyewa daga bisani su fitar da ita kasashen ketare.

Bayan zuwa kasuwar yan chanjin da jami’an na EFCC su ka yi hukumar ta sake aike da jami’an ta Filayen Jiragen sama na Jihar Kano da Legas da kuma garin Part Horcort domin damke masu shirin fita da dalar kasahen ketare.

Hukumar ta EFCC ta tura jami’an ne sakamakon faduwar farashin Naira da aka yi a Jiya Alhamis wanda ba a taba samu ba, yayin da ita kuma dala daya ta kai Naira 705 a kasuwar chanji.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Ministar Masana’antu Za Ta Halarci Taron Zuba Hannun Jari A Burtaniya

Published

on

Ministar masana’antu da ciniki da zuba hannun jari ta Kasa Doris Nkiruka za ta halarci gurin taron zuba jari na ‘yan Najeriya mazauna Kasashen ketare NDDIS a kasar Birtaniya, tare da gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani.

A yayin taron ministar ce za ta kasance babbar bakuwa ta musamma a gurin, yayin da shi kuma gwamnan Jihar ta Kaduna zai kasance babban bako mai gabatar da jawabi.

Taron wanda aka yi masa take da Invest Nigeria Invest Africa, za a gudanar da shi ne dai a ranar 24 ga watan Mayun da muke ciki a birin Londan.

Daga cikin mahalarta taron sun hada da babbar mai ba shugaban kasa shawara kan samar da ayyukan yi da kananan sana’o’i, Temitola Emitola, da shugabar ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare Hon Abike Dabiri Erewa, a cikin wata sanarwar da daraktan yada labarai ta kungiyar Lady Doyin Ola ta fitar.

Taron zai kuma kara samun halartar shugabannin ‘yan kasuwa na kasashen ketare da na kasashen Afirka da Birtaniya da kuma kasashe rainon Ingila da sauran masu zuba hannun jari.

Continue Reading

Labarai

Ƴan Sanda Sun Kashe Ƴan Bindiga Biyu A Kaduna

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da hallaka wasu ‘yan bindiga biyu a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar na Jihar Mansir Hassan ya bayyana faruwar lamarin a ranar Lahadi.

Mansur ya ce jami’an nasu sun hallaka ‘yan bindigar ne bayan sun hallaka wani manomi a gonarsa sa ke kauyen Kuriga a Jihar a ranar Asabar.

Kakakin ya kara da cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na safiya,bayan ‘yan bindigar dauke da makamai suka hallaka  mutumin mai suna Isiyaka Mikailu mai shekara 60 a garin Kuriga a gonarsa.

Mansu ya ce bayan samun labarin faruwar lamarin suka aike da jami’ansu hadi da mafarauta zuwa gurin da lamarin ya faru.

Jami’in ya ce bayan zuwan jami’annasu gurin sai da suka yi musayar wuta da maharan, har ta kai ga sun hallaka biyu daga cikinsu.

Kakakin ya ce a yayin harin jami’an sun kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu da harsasai guda 17 daga hannun maharan.

Continue Reading

Labarai

Ƙungiyar Kwadago Za Ta Jalarci Tattaunawa Da Gwamnatin Tarayya

Published

on

Kungiyoyin kwadago ta Kasa NLC da Takwararta ta TUC sun bayyana cewa a gobe Talata za su sake halartar zaman ci gaba da tattauna akan sabon mafi karancin albashin ma’aikatan kasar da kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa kan batun.

 

Mataimakin shugaban kungiyar TUC ta manyan ma’aikatan kamfanoni da masana’antu Mista Etim Okon ya tabbatar da kudurin kungiyoyin a yau Litinin a Abuja.

 

Kungiyoyin za su sake halartar taron tattaunawar ne bayan wasikar da kwamitin da gwamnatin ta kafa ya sake aike musu a ranar Asabar.

 

Kungiyoyin za su sake zaman ne domin ciumma matsaya akan sabon mafi karacin albashin ma’aikatan kasar, wanda kungiyoyin ke nema a biya ma’aikatan naira 615,000.

 

A zaman baya da aka gudanar kwamitin da gwamnatin ta kafa ya shaidawa kungiyoyin kudurin gwamnatin na fara biyan ma’aikata naira 48,000 a matsayin mafi karancin albashi ma’aikata, inda kungiyar ta yi watsi da batun.

 

A sanarwar da Kungiyar NLC ta fitar ta gargadi gwamnatin da kada ta yi musu tayin Naira 100,000 a matsayin mafi karancin albashi.

 

Shugaban sashin yada labara na NLC Benson Upah ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

Sanarwar ta ce su na fatan gwamnati za ta dauki batun da muhimmaci na biyan mafi karancin albashi na naira 615,000.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: