Gwamnatin tarayya ta ce ba ta ti ƙarin farashin man fetur ba kamar yadda wasu gidajen mai ke siyar das hi sama da 165.

Ƙaramin ministan man fetur ne ya bayyana haka a ranar Litinin a Abuja yace wasu daga cikin dilallan man fetur ne su ka ƙara farashi da su ke siyar da litar man daga naira 170 zua sama.
Ya ara da cewar gwamnatin bat a da shirin ƙara farashin man a halin yanzu kuma dukkanin hukumomin das u ka shafi ɓangaren man fetur na yin duk mai yuwuwa don ganin an shawo kan matsalar wahalarsa da ake ciki.

Ya ƙara da cewar gwamnati bat a jin daɗin yadda dillalan man fetur ke ƙara farashin wanda hakan ya sanya ake siyansa da tsada duk da cewar akwai shi a wasu gidajen man.

Sannan aikin ƙara farashin man fetur da wasu dillalan man ke yi babu sanin gwamnati sannan bat a sahalewa dilallan hakan ba kuma za su yi ƙoƙarin anin sun kawo ƙarshen wahala da tsadarsa.
Fiye da watanni biyu aka shafe ana fama da ƙarancin man fetur wanda hakan ya sa wasu dillalaln man ke ƙara farashi litar man.
Sai dai a ɓangaren masu gidajen man sun bayyana yadda aka ƙara musu haraji da kuma wahalar samun man da daɗewarsa kafin shigo das hi a matsayin dalilin day a sa su ka ƙarawa litar fetur kuɗi.
Idan ba a manta ba kayayyakin amfain yau da kullum na ci gaba da ƙara hauhauwar farashi musamman ɓangaren abincin, man fetur, gas din girki, gas ɗin amfani da mota da sauran kayan amfani na gida da kasuwa.
Wasu na alaƙanta tashin farashin wasu kayayyakin da hauhawar farashin dala wanda ya sanya darajar naira ke ci gaba da yin ƙasa musamman a kasuwar chaji ta bayan fage.F