Gwamnatin Jihar Borno ta bayyana cewa dukkan alkalin kotun shari’ar musulunci da aka samu da hannu wajen yin almundahan ko tauye hakki za a sauke shi daga bakin aiki.

Babban Alkalin Jihar Mai shari’a Kashim Zannah shine ya tabbatar da hakan a yayin da ya ke bai wa sabbin Alkali 21 a Jihar rantsuwar kama aiki a jiya Talata a kotun shari’ar musuunci.

A yayin jawabin Kashim Zannah ya bayyana musu cewa dukkan wanda aka samu gurin yin zalinci to tabbas za a kore shi daga bakin aiki baki daya.

Kashim ya buƙaci alƙalan su kasance gurin yin gaskiya da adalci a dukkan wata shari’a da za su gudanar.

Zannah ya ce cancantar su ce ta sanya aka dauke su aiki tare da bin duk wasu ka’idoji da su ka dace, inda ya ce ba za su lamunci yin almundahana ba ko cin zarafi a cikin aikin su ba.

Kashim Zannah ya kara da cewa da zarar gwamnatin Jihar ta kammala samar da kayan aiki a sabbin wuraren da gwamnatin ta samar, za a tura sabbin alkalan za su fara gudanar da ayyukan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: