Wasu yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun hallaka dogarin mataimakin sufeton yan sanda na ƙasa AIG Audu Madaki tare da hallaka dogarinsa.

Audu Madaki mataimakin sufeton yan sanda ne da kula da shiyya ta 12 a jihar Bauchi.

An kai musu hari ne a yayin da suke tsaka da tafiya a tsakanin garuruwan Barde da Jagindi a Kaduna.

Al’amarin ya faru ne ranar Talata da misalin karfe 02:30pm na rana.

Rahotanni sun nuna cewar an harbi mataimakin sufeton yan sandan tare da yi masa rauni sai dai tuni aka kaahe dogarinsa.

Wata majiya daga shiyya ta 12 a Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai mai magana da yawun ƴan sanda shiyya ta 12 a Bauchi Thomas Goni bai tabbatar da faruwar lamarin ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewar an aike da jami’an yan sanda cikin daji domin zaƙulo mutanen da su ka kai harin.

A sakamakon yawaitar hare-hare da zaman ɗar-ɗar a Abuja babban sufeton yan sandan na kasa ya bayar da umarnin ƙara aike da jami’an domin tabbatar da zaman lafiya a Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: