
Rundunar ƴan sandan Najeriya za ta fara wani sumame na musamman a dazuka da gidajen da babu kowa a ciki da wajen babban birnin tarayya Abuja.
Ƴan sandan Abuja sun ɗauki matakin ne a wani salo na kara tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin al’aumma.

Mai.magana da yawun yan sandan Abuja Josephene Adeh ce ta tabbatar da hakan a jiya Laraba.

Gidan talabiji na Channels ya ruwaito cewar ƴan sandan sun musanta batun cewar ƴan bindiga na fakewa a cikin garin Abuja.
Ta ce a halin da ake ciki an kara yawan jami’an tsaro a Abuja kuma hakan ya biyo bayan umarnin sufeton yan sanda na kasa.
Sannan za su samar da bayanan sirri a kan sha’anin tsaro a Abuja tare da ƙaddamar da sumamen a ciki da dazukan Abuja.
Aikin samar da tsaron zai fara ne bayan rahotanni da aka samu cewar ƴan bindiga na shirin kai munanan hare-hare babban binrin tarayya Abuja da wasu jihohin Najeriya.