Ƴan jam’iyyar adawa a majalisar tarayya sun sake jaddada aniyarsu na yunkurin tsige shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Wakilai a zauren majalaisar sun tabbatar da cewar muddin shugaban kasar ya gagara shawo kan matsalar tsaro, ‘yan majalisar sun ce ba za su fasa tsige shi ba.

Sanata Francis Fadahunsi mai wakiltar gabashin Osun a jam’iyyar PDP yace ba gaskiya ba ne a rika cewa sun ja baya daga yunkurin sauke shugaban kasar.

Fadahunsi ya tabbatar da cewa Sanatocin adawa ba su janye wannan yunkuri da su ja dauko ba.

Sanatan yace har wasu daga wakilai ‘yan majalisar Arewa na goyon bayansu na tsige shugaban.

Sanata Danjuma La’ah guda a zauren majalisar dokokin ƙasa yace wa’adin da suka ba gwamnati na makonni shida na nan.

Wani ‘dan adawa a majalisar dattawa, Nicholas Tofowomo ya shaida cewa iyakar saninsa shi ne har yanzu maganar tsige shugaban kasa tana nan.

Sanata Nicholas Tofowomo yace da an dakatar da yunkurin, da shugaban marasa rinjaye ya sanar da su duk da cewa yanzu ‘yan majalisar sun tafi hutu.

Sanatan na jihar Ondo yake cewa kafin su janye maganar, sai an tattauna da su, kuma a iyaka saninsa, har zuwa yanzu ba ayi hakan ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: