Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce dakarunta sun kama wani Soja mai ritaya ɗan shekara 90 bisa zargin kai wa yan bindiga miyagun kwayoyi.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya ce mutumin mai suna Usman Adamu, ya shiga hannusu ne a Mailalle, ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato.

Kakakin hukumar ya ci gaba da cewa an kama wanda ake zargin ɗauke da hodar Iblis mai nauyin Kilo 5.1kg.

Babafemi ya ƙara da cewa a wata nasarar ta daban da hukumar ta yi, dakarun sun kama wani, Anietie Okon Effiong, wanda aka gano Malamin Coci ne kan zargin hannu a shigo da wata kwaya daga ƙasar Indiya.

Ya ƙara da cewa wani ɗan asalin ƙaramar hukumar Ovia a jihar Edo dan kimanin shekara 37 a duniya mazaunin ƙasar Italiya Solo Osamede, ya shiga hannun jami’an ranar 30 ga watan Yuli.

An kama mutumin ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas kan dauko ƙunshin tabar Heroic guda 41.

Ya ce matashin ya shiga hannu ne yayin da yake kokarin hawa jirgin saman Turkish Airline zuwa birnin Milan na ƙasar Italiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: