Jami’an ƴan sandan jihar Legas sun bindige wasu ‘yan fashi guda biyu da ake zargin suna addabar mazauna yankin Apapa, Ajegunle da kewaye.

Rahotanni sun cewa a ranar 4 ga watan Agusta, ‘yan bindigar sun mamaye wani yanki tare da korar wasu mazauna garin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya wallafa a shafin Twitter, ya ce an gano maboyar ƴan fashin ne daga bisani aka yi musayar wuta da su.

Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan sandan sun bi sawun ‘yan ta’addan zuwa maboyarsu da ke Ajegunle, inda aka yi artabu da bindiga.

Ya ce, an gano maɓoyar ƴan fashin a Area B unguwar Apapa kuma jami’an usu ka samu nasarar kashe biyu daga ciki yayin da wasu su ka tsere.
‘Yan fashin da aka hallaka sun daɗe ana nemansu ruwa a jallo, yayin da guda daga cikinsu ma bai daɗe da fitowa daga gifan gyaran hali ba.