Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce mutane 670 ake zargi sun kamu da cutar kyandar biri yayin da huɗu su ka rasa rayuwarsu.

Hukumar ta ce an tabbatar da cutar a kan mutane 157 yayin da ake zargin mutane 413 su na ɗauke da cutar a tsakanin jihohi 25 na ƙasar da babban birnin tarayya Abuja.

Mutanen da su ka mutu sun fito ne saga jihohin Legas, Ondo, Akwa Ibom da jihar Delta.’

Jihohin da aka samu masu ɗauke da cutar sun hada da Taraba mutane 5, Adamawa mutane 13, Bayelsa mutane 12, Legas mutane 20 Ondo mutane 14  sai jihar Rivers da aka samu mutane 11.

Sauran jihohin da aka samu masu cutar akwai Edo Nassarawa Filato, Anambra Kwara Kano,, Imo da babban bhirnin tarayya Abuja.

Haka kuma an samu masu cutar a jihohin Neja, Cross River, Borno, Oyo, Abia, Gombe, Katsina, Kogi, Ogun, Bauchi, A bia, Imo da jihar Akwa Ibom.

Dukkanin mutanen an samu rahoton ne a shekarar 2022 da mu ke ciki.

Sannan a tsakanin ranar 25 ga watan Yuli zuwa 31 ga watan Yuli n samu masu cutar mutane 24 masu ɗauke da cutar.

Hukumar ta bayyana wasu alamomi da su ke nuna masu cutar daga ciki akwai Ciwon kai, ciwon jiki, zazzaɓi da kasa sai ƙuraje, tare da shawartar masu zargin sun kamu da cutar da u hanzarta zuwa ga ma’aikatar lafiya mafi kusa domin duba lafiyarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: