Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana yunkurin tsige shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da wasu yan majalisa suka yi da wani lamari abun takaici.

Adamu ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da kafar talabijin ta Trust TV yau Talata, 9 ga watan Agusta, 2022 a birnin tarayya Abuja.

Abaya an kawo rahoton cewa yan majalisun tarayya sun yi barazanar fara bin matakan tsige shugaban ƙasa daga kujerarsa a wani taron manema labarai jim kaɗan kafin tafiyar su hutun watanni biyu.

Mambobin majalisar sun yanke wannan hukuncin ne bayan sun baiwa shugaban ƙasan wa’adin makonni Shida ya shawo kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan.

Da yake maida maryani kan batun, shugaban APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Adamu ya ce yunkurin babban abun takaici ne, wanda ya bar kan turba mai kyau.

Ya ce Shirin shige shugaban ƙasa babban abun takaici ne da babu shi kwata-kwata yanzu. Tare da majalisar tarayya, suna tsammanin irin haka, yana faruwa a ko ina a kowace demokaraɗiyya.

Da yake martani kan yajin aikin Malaman Jami’o’i da kokarin jam’iyya mai mulki na ganin ɗalibai sun koma azuzuwan su, Adamu ya ce APC ta yaba kwarai da yadda iyaye da ɗalibai ke nuna damuwar su.

Ya kuma yi fatan cewa ƙungiyar ASUU zata “dawo cikin hayyacinta a zahirance” ta dawo kan teburin sulhu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: