Kwamandan hukumar kare fararen hula ta Civil Defence a Najeriya Abubakar Audi ya yi taron gaggawa da jami’ansa don duba halin tsaron ƙasar.

Shugaban ya gayyaci kwamandojin hukumar na shiyya daban-daban na ƙasar domin ganawa da su a helkwatar hukumar da ke Abuja.

Taron da shugaban ya kira ana sa ran ya mayar da hankali ne a kn sabbin matakai da hukumar ta ɗauka domin aikin tsaron da ya rataya a wuyanta.

An gayyaci manyan jami’an hukumar na jihohi daban-daban tare da sanar da su sabbin dabarun aiki da kuma hanyar d za  ƙara ƙarfafa  tsaro.

Wannan na zuwa ne bayan da majalisar dokokin Najeriya ta gayyaci manyan shugabannin tsaro domin bibiya a kan yunƙurin kai wasu hare-hare Abuja da wasu jihohin Najeriya.

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne na shirin kai hare-hare wasu jihohin ƙasar ciki har da jihar Legas da babban birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: