Yayin da ake ci gaba da ganin tabarbarewar tsaro a kasar nan, babban hafsan sojin kasa, Janar Lucky Irabor ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a gudanar da babban zaben 2023 cikin lafiya.

‘Yan Najeriya sun nuna damuwar ko za a yi zaben 2023 ganin yadda lamurran tsaro da karuwar hare-haren ‘yan ta’adda ke kara ta’azzara.

Da yake magana a yayin wani taron manema labarai a yau Talata a hedkwatar tsaro da ke Abuja, Janar Irabor ya ce sojoji za su yi duk mai yiwuwa don ganin cewa babu abin da ya hana gudanar da zaben.

Babban hafsan tsaron ya kuma nanata kudurin sojojin Najeriya na kare manufofin dimokaradiyya a kasar da ta fi yawan al’umma a Afirka.

A cewarsa, sojoji sun yi alkawarin kare dimokuradiyyar Najeriya kuma ba za su canza daga matsayin ba.

An yi taron ne domin neman goyon bayan kungiyoyin yada labarai don tunkarar kalubalen tsaro a kasar, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Wannan dai shi ne karo na biyu a jerin tattaunawa tsakanin babban hafsan hafsoshin tsaron kasar da shugabannin zartarwa da editocin kungiyoyin yada labarai a Najeriya.,

Leave a Reply

%d bloggers like this: