– A karshen makon da ya gabata ne hukumar NSCDC a jihar Sokoto ta gabatar da wasu ‘yan bindiga guda biyu da suka addabi kananan hukumomin Silame, Binji, Gudu, Tureta da Dange/Shuni na jihar.

Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar rundunar NSCDC na Sokoto, kwamandan jihar, Muhammad Dada, ya ce Alhaji Koire da Alhaji Buba ’yan fashi ne masu hadari dake da yan bindiga sama da 300 a sansaninsu.
Muhammad ya ce, su biyun sun addabi mutanan kananan hukumomin Silame, Binji, Gudu, Tureta da Dange/Shuni na jihar.

Ya ce Manyan ‘yan bindiga dake gudanar da ayyukansu a Jamhuriyar Nijar da Najeriya musamman yankin Koire, sun tsere daga kamun jami’an tsaro ta hanyar amfani sihiri.

Mohammed yace a Lokacin da ya samu labarin inda suke a karamar hukumar Silame, shi da kanshi ya jagoranci mutanen sa kuma bayan kwashe kwanaki biyu a cikin daji suka yi nasarar kama su.
Bayan kama su, ‘yan ta’addam suka yi yunkurin ba su cin hancin N10m domin a bar su su gudu.
A nasa jawabin, Alhaji Buba, ya ce yana da hannu wajen yin garkuwa da mutane a Dabegi da ke karamar hukumar Dange/ Shuni inda suka karbi kudin fansa naira miliyan hudu da kuma Kudula da ke karamar hukumar Gudu inda suka karbi kudin fansa naira miliyan daya.
Ya bayyana cewa suna da wani shugaba a jamhuriyar Nijar mai suna Danbuzu wanda ya kawo musu bindigogi kirar AK-47 da alburusai.