Kwamitin majalisar dattijai mai kula da asusun gwamnati ya soki hukumar kula da asusun inshorar jama’a ta Najeriya NSITF bisa zargin karkatar da naira biliyan 17.158.

Ma’aikatan NSITF na baya da na yanzu sun bayyana a gaban kwamitin a ranar Juma’a don kare tambayoyin da aka yi wa hukumar a cikin rahoton tantancewar na shekarar 2018.

Rahoton binciken ya ce hukumar NSITF ta karkatar da naira biliyan N17.158 daga asusun bankin Skye da First Bank zuwa asusu daban-daban na mutane da kamfanoni daga watan Janairu zuwa Disamba na shekarar 2013.

Sai dai babu wani daga cikin ma’aikatan gudanarwa na hukumar na baya da na yanzu da zai iya bayar da gamsasshen bayani kan yadda aka kashe kudaden.

Wadanda ke jagorantar al’amura a shekarar 2013 sun shaida wa kwamitin cewa sun bar takardun da ke ɗauke da bayanan a hannun ma’aijatar bayan barinsu aiki, yayin da Manajan Daraktan NSITF na yanzu, Michael Akabogu, ya ce babu irin wadannan takardu a hannunsu.

Sannan ya musanta batun cewar ruwan sama ya lalata takardun wanda ya ce babu wasu kwari da su ka lalata wasu takardu da su ke da muhimmanci a wajensu.

Yayin da ya ke nasa jawabin, Manajan Daraktan NSITF daga shekarar 2010 zuwa shejarar 2016, Umar Munir Abubakar, ya ce bai da masaniya kan wannan tambaya, kuma ba shi da wani bayani a kai tunda ba a gudanar da tantancewar ba a lokacin sa.

Sai dai magajinsa, Adebayo Somefun, wanda shi ne shugaban hukumar daga watan Mayun shekarar 2017 zuwa watan Yulin shekarar 2020, ya ce wadanda ke sashen asusu ne kadai za su iya gano takardun da Babban Manajan Kudi na yanzu.

Ya yi zargin cewa an kulle su a cikin wani banki da wata kwantena da aka yi watsi da su a harabar ofishin NSITF da ke Abuja.

Mambobin kwamitin sun soki jami’an kan gazawar da suka yi wajen bayar da hujjar kashe makudan kudade tare da wasu shaidu, sai dai an umarce su da su sake bayyana ranar 22 ga watan Satumba da takardun da ake bukata domin bayar da isasshiyar hujja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: