Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ana bukatar kidayar jama’a a shekarar 2023 domin tunkarar kalubalen tsaro a kasar, domin hakan zai ba da cikakken bayani kan yawan al’ummar kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki na kasa kan kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023 da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja.

Ya ce al’ummar kasar na bukatar sabbin bayanai da aka tsara ba wai kawai aiwatar da manufofin kasa da aka kaddamar kwanan nan kan yawan jama’a don ci gaba mai dorewa da sauran manufofin gwamnati ba har ma da wasu tsare-tsare na rage radadin talauci da karfafawa matasa.

Ya ce samar da fasahar zamani a cikin kidayar yawan jama’a da gidaje na 2023 zai tabbatar da inganci da daidaito a cikin alkaluma, sannan kuma Najeriya za ta iya zama matsayi na uku a duniya nan da shekarar 2050, bayan ƙasashen China da Indiya.

Najeriya mai yawan jama’a 216,783,381, ita ce kasa ta shida mafi yawan jama’a a duniya kuma kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka.

Ya ce saboda yadda yawan jama’a ke karuwa cikin sauri da kuma yawan matasa, ana kuma hasashen ƙasar za ta kasance kasa ta uku mafi yawan mutane a duniya nan da shekara ta 2050.

Leave a Reply

%d bloggers like this: