Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU ta ce gwamnatin Najriya ba ta shirya kawo ƙarshen yajin aikin da su ke ciki ba.

ƙungiyar ta alaƙanta hakan da abin kunya sakamakon shafe kusan watanni shida su na yajin aikin amma gwamnatin ta gaza kawo ƙarshen sa.

Shugaban ƙungiyar Emmanul Osodoke ne ya sanar da haka a wani shiri da aka gabatar tare da shi a gidan talabiji na Channels.

Ya ce romon baka gwamnatin ke yi wa ƴan ƙasar amma babu wata cikakiyar matsaya da ta ɗauka don ganin an kawo ƙarshen yajin aikin.

Ganin yadda al’amuran ke tafiya, shugaban yace ba za su gajiya ya sa su janye daga yajin aikin da su ke ciki ba har sai an dawo da ƙimar karatu a mkarantun jami’a.

Ya ƙara da cewa a shirye su ke su tabbatar sun koma bakin aikinsu muddin aka cika musu alƙawuran da su ke nema daga gwamnatin.

Shugaban ƙungiyar ya ce gwamnati ba da gaske ta ke ba don ganin ta kawo ƙarshen yajin aikin da su ke ciki.

Fiye da watanni shida ƙungiyar ta fara yajin aiki domin neman biyan buƙatunsu daga gwamnatin wanda hakan ya haifar da tsaiko ga karatun ɗaliban jami’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: