Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a Maiduguri babban birnin jihar Borno domin ƙaddamar da wasu manyan ayyuka a jihar.

Shugaban ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama a yau Alhamis a ziyarar aiki ta kwana guda da ya kai jihar domin ƙaddamar da muhimman ayyuka.
Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum da mataimakinsa na aga cikin waɗanda su ka tarbi shugaban a filin jirgin sama.

A na sa ran shugaban zai ƙaddamar da ayyukan gidajen malamai, da wasu gidaje da gwamnati ta gina domin amfanin maa’aikata a jihar.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar ministar jin ƙai Hajiya Sadiya Umar Farouƙ da ɗan takarar mataimakin shugaban kasa da wasu manyan muƙarraban gwamnati.
Sannan daga ciki akwai wasu daga cikin wakilai a zauren majalisar dattawan Najeriya da wasu daga majalisar wakilai ta tarayya.
A na sa ran shugaban zai koma Abuja ranar Juma’a bayan kammala ƙaddamar da ayyuka a jihar.