Kwamitin da aka kafa a Majalisar wakilan tarayya domin bincike a kan tallafin man fetur ya fara aiki a birnin tarayya Abuja.

Gidan rediyon FRCN ya ruwato cewa kwamitin na musamman ya fara yin zama da Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed a majalisa.
Da aka gayyaci Ministar a gaban kwamitin domin tayi karin haske, ta shaida cewa gwamnatin tarayya na biyan naira 283 a matsayin tallafi a duk litar mai.

Jawabin da ministar ke nufi shi ne duk rana sai tallafin man fetur ya ci wa gwamnati naira biliyan 18.397.

A shekara mai zuwa, gwamnati tayi hasashen kullum za a rika shigo da lita kusan miliyan 65 na man fetur wanda asalin farashin litan ya kai naira 448.
Idan aka yi lissafi da farashin da ake saidawa mutane fetur a kasuwa a kan N165, hakan na nufin gwamnati za ta cika gibin N283.2k da za a samu a kowacce lita.
Sannan idan aka yi lissafin wannan kudi a yadda farashin Dalar Amurka take a yau, za a gane a duk shekara gwamnatin za ta rika batar da naira tiriliyan 6.5.
Ministar ta ce daga watan Junairu zuwa Disamban shekara mai zuwa, za a kashe naira tiriliyan 6.715 a wajen biyan tallafin fetur ga ‘yan kasuwa.