A wani labarin kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙas NEMA ta tabbatar da lalacewar yankuna 225 a tsakanin jihohi biyu na Arewacin Najeriya.

Shugaban hukumar mai kula da shiyyar Kano da Jigawa ya Daktya Nuradden Abdullahi ne ya tabbatar da hakan ya ce ƙididdiga ce daga watan Yuli zuwa watan Agusta.

Ya ce lamarin ya shafi ƙananan hukumomi 31 da su ke a jihohin Kano da Jigawa.

Ƙananan hukumomin na Kano su ke Gwale, Albasu, Rimin Gado,  Ajingi, Tudun Wada, Tsanyawa, Rimin Gado, Kibiya, Doguwa, Ƙiru, Dawakin Kudu, Ɗanbatta Shanono da ƙaramar hukumar Ɓagwai.

Ƙananan hukumomin da su ka shafa a jihar Jigawa su ne Birnin Kudu, Gwaram, Kafin Hausa, Malam Madori, Haɗeja, Guri, Birniwa, Jahun, Auyo, Kiyawa, Kaugama, ɓaɓura, Kiriksamma,Miga, Jahun da Dutse bbban birnin jihar.

Shugaban ya ce lamarin ya shafi gonaki da ama da kuma gidaje wanda hakan ya tilasta raba da dama daga muhalinsu.

Ya ƙara da cewar da yawan mutane da ke yankunan sun rasa matusgansu tare da neman mafaka a wasu wuraren daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: