Rundunar ƴan sanda a jihar Nassarawa sun tabbatar da kuɓutar kwamihsinan yaɗa labarai na jihar wanda aka yi garkuwa da shi a ranar litinin.

An yi garkuwa da Yakubu Lawal a gidansa da ke ƙaramar hukumar Nassarawa-Eggon a daren Litinin.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Ramhan Nansel ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a.

Ƴan sanda a jihar sun ce har yanzu ba su kama ko da mutum guda da su ke zrgi da hannu wajen yin garkuwa da kwamishinan ba.

Sai dai sun ce za su ci gaba da gudanar da bincike domin kama waɗanda aka ke da hannu a ciki.

Sai dai ƴan sandan ba su bayar da bayani ko sun samu tabbacin biyan kuɗin fansa daga iyalan kwamihsinan ba kafin sakinsa.

Amma sun tabbatar da cewar za su yi ƙoƙari a ɓangarensu wajen ganin sun gano mutanen da ke da hannu wajen sace kwamishinan.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2021 sai da yan bindiga su ka taɓa yin garkuwa da kwamishinan yaɗa labarai a jihar Neja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: