Yan sanda a jihar Yobe sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kashe wani limami a jihar.

An hallaka Goni Aisami a kan hanyarsa ta Nguru zuwa Gashua ranar Juma’a da daddare .
Waɗanda aka kama ana zargin sojoji ne da ya rage musu hanya su ka hallakashi da bindiga.


Sai dau ƴan sanda ba su tabbatar da ko sojojin ne su ka hallakashi Baa.
Mai magana da yawun yan sandan jihar ya ce an hallaka mutumin ta hanyar amfani da bindiga kirar AK47.
Jami’an sa kai na Jaji-Maji sun yi kokarin gano gawar malamin bayan yan bindigan sun gudu da motarsa.
Gwamnan jihar Maimala Buni ya nuna takaicinsa a dangane da kisna babban malamin.
Sannan ya sha alwashin tabbatar da adalci ta hanyar tsayawa don ganin an hukunta wadanda ke da hannu a ciki.