Hukumar kula da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce cutar Ƙyandar Biri na ci gaba da bazuwa a Najeriya yayin da ta shiga jihohi 26 da babban birnin tarayya Abuja.

Makon farko na watan Agustan da mu ke ciki mytane 60 aka samu daga cikin jihohin ƙasar.

Adadin da aka samu ya ninka da kashi ɗari la’akari da ƙididdigar da ake fitarwa mako-mako a watan baya.

Ƙasa da wata guda cutar ta sake tsallakawa jihohi 15 na Najeriya yayin da ake ci gaba da samun masu ɗauke da cutar da kuma wasu da ake zargi sun kamu.

Cutar Ƙyandar Biri ta fara ne a Najeriya tun a shekarar 2017 sai dai zuwa yanzu ta fi saurin yaduwa a cikin jama’a.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce a halin yanzu cutar Ƙyandar Biri ta fi mayar da hankali a kai ganin yadda ta ke ci gaba da shiga ƙasashen duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: