Connect with us

Labarai

Manoma Na Kokawa A Kan Harin Yan Bindiga Duk Da Sulhun Da Su Ka Yi A Neja

Published

on

Manoma a kananan hukumomin Shiroro, Munya da Rafi a jihar Neja sun shiga damuwa yayin da suke fara shirin girbin amfanin gonakansu.

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna yadda manoman su ka shiga tashin hankali kan warware yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga suka yi a daidai lokacin da tumatir masara da rogo suka nuna.

An sace manoma 16 tsakanin ranakun Asabar da Lahadin karshen makon jiya a kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jihar.

A cewar manoman, ‘yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare kan jama’a duk da cewa a baya sun yi da wajewar zaman lafiya a lokutan shuka.

Majiya daga karamar hukumar Rafi ta ce, ‘yan bindigan sun yi awon gaba da limamin garin Luga, a karamar hukumar da sanyin safiyar ranar Lahadi yayin wani kazamin hari.

Shugaban majalisar matasan Lakpama, Jibrin Abdullahi Allawa ya bayyana cewa, an kuma sace wasu manoma 15 daga yankunan Bassa da yammacin Asabar.

Ya ce, jama’a da dama, ciki har da mata da kananan yara ne suka yi gudun tsira daga harin ‘yan bindiga.

Jihar Neja ta shafe shekaru ta na fuskantar hare-haren yan bindiga duk da cewar gwamnati na nuna ta na samun nasara a yaki da su.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Mai Maganin Gargajiya Ya Harbi Kansa Bayan Yin Gajin Maganin Bindiga

Published

on

Wani mai maganin gargajiya mai suna Ismail Usman ya harbi kansa a lokacin da yake gwajin maganin bindiga a yankin Kuchibiyi da ke Karamar Hukumar Bwari a birnin Abuja.

Wani mazaunin Kuchibiyi Samson Ayuba ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, a lokacin da mutumin ya ke kokarin gada ingancin maganin bindgar da ya hada.

Ya ce sai dai bayan faruwar lamarin an yi gaggawar kai shi asibitin gwamnati da ke Kubwa bayan ya fadi, inda kuma ya samu raunuka.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin na Abuja Joesephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ta fitar.

Adeh ta ce sun samu rahotan cewa wani mai maganin gargajiya ya harbe kansa a lokacin da yake gwajin maganin bindigar da ya hada.

Sai dai ta ce sakamakon munanan raunukan da ya samu aka kai shi asibitin Kubwa domin duba lafiyarsa, daga bisani kuma aka mayar da shi asibitin kwararru da ke Gwagwalada domin kara samun kulawa.

Kakakin ta kara da cewa abinciken da aka gudanar a gidansa an gano wata bindigar gargajiya da layu wadanda ya yi amfani da su gurin gwajin maganin bindigar.

Adeh ta ce a halin yanzu su na ci gaba da gudanar da bincike kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar makami ba bisa ka’ida ba tare da yunkurin hallaka kansa.

 

Continue Reading

Labarai

Jami’an Soji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 100 A Sassan Najeriya A Mako Guda

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta ce jami’anta sun samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda 135, tare da kama mutane 185 da ake zargi da aikata laifuka, da kuma ceto mutane 129 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na fadin Kasar nan a cikin mako guda.

Daraktan yada yada labaran hedkwatar tsaro ta Kasa Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan ne a yau Asabar a hedkwatar da ke Abuja.

Buba ya ce daga cikin wadanda aka kama ciki harda 61 da ake zargi da satar mai.

Acewar Buba ‘yan ta’adda a yankin Arewa ta tsakiya sun fara mika wuya ga sojojin su.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Mayarwa Da Jami’ar Yusuf Maitama Sule Asalin Sunanta

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta mayarwa da Jami’ar Yusuf Maitama Sule tsohon sunanta na asali.

Majalisar Zartarwar jihar ce ta dauki matakin mayarwa da Jami’ar tsohon sunanta, bayan wani taro da gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a jiya Juma’a.

Idan ba a manta ba dai a watan Yulin shekarar 2017 ne tsohon gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya canjawa jami’ar suna zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule, domin tunawa da marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule, bisa irin gudummawar da ya bai’wa Jihar, dama Kasa baki daya.

 

Sai dai kuma a halin yanzu gwamnatin Jihar mai ci karkashin Jam’iyyar NNPP ta dauki matakin dawowa da Jami’ar tsohon sunanta.

Northwest University ya samo asali ne a zamanin mulkun tsohon gwamnan Jihar Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya samar da ita.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: