Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama tarin miyagun kwayoyi da suka haura miliyan 2.3 da aka nufi kai wa jihohin Arewa.

Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin hukumar, Femi Babafemi a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi.

Kakakin ya bayyana cewa, jihohin da za a kai kayayyakin su ne kamar haka, Borno, Kano, Kaduna, Sokoto, Zamfara, Gombe, da Nasarawa.

Ya kuma bayyana cewa, an kama miyagun kwayoyi ne a yankunan Kaduna, Kogi, Sokoto, da kuma babban birnin tarayya Abuja a makon da ya gabata.

A ranar 12 ga watan Agusta, an kama Umar Sanusi a wani sumame a Kaduna, an kuma mayar da shi Kano inda aka kama shi da wasu kayan maye masu yawa.

Haka zalika, an kama kwalabe 7,068 a wata mota da aka shirya kai wa Kaduna, Zamfara, Gombe, Kano da Borno.

Sannan an kama wani Abubakar Ahmad a Zamfara, an kama kwalabe 285 na NPS a ranar 13 ga watan Agusta.

A jihar kogi kuma, an kama kwayoyi 696,000 na Tramadol da Exol-5 da aka dauko daga Anambra inda za a zarce da su jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya.

A ranar 19 ga watan Agusta, hukumar ta kame 300,000 na kwayar Diazepan a kan titin Okene zuwa babban birnin tarayya Abuja a wajen wani Faruku Bello mai shekaru 30.

A babban birnin arayya Abuja da wasu yankuna a jihar Anambra, an kama kwayoyin 323,200 masu girman 225mg da aka yi niyyar kai wa jihar Nasarawa da ke makwabtaka da Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: