Hukumar fansho ta kasa ta bayyana fushinta game da yadda ma’aikatan gwamnati masu ritaya da dangin da ke ba da rahoton mutuwar karya domin tunkarar gwamnati da sunan karbar kudin fansho.

Hukumar ta ce za ta dauki matakai masu tsauri kan wadannan mutane kamar yadda doka ta tanada.

PenCom ta dauki matakin cewa, bayan gabatar da shaidar mutuwa gareta, dole ne bankuna su rufe asusun mamaci domin tabbatar da ya mutu kafin a fara maganar hakkinsa na hannun hukumar.

Hukumar ta ce ta damu matuka da yadda ake yawan samun mutuwar karya daga tsoffin ma’aikata da danginsu.

Shugaban sashen hakkokin ma’aikata da inshora a PenCom, Obiora Ibeziako, ne ya bayyana damuwa yayin da yake zantawa kan yadda ake karbar hakkokin ritaya da kudaden fanshon ma’aikata.

Ya ce Yan Najeriya sai mutuwa suke suna dawowa, idan ka turo da sanarwar mutun ya mutu, za su tabbatar da hakan ta hanyar sanar da bakinsa su garkame asusun mutum.

Leave a Reply

%d bloggers like this: