Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa kungiyar ASUU ba ta da wani dalilin da zai sanya ta ci gaba da gudanar da yajin aikin da ta ke yi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin taron ganawa da manyan Sakatarori da Daraktoci da shugabannin ma’aikatu da na kananan hukumomi a dakin taro na Sir Ahmad Bello da ke Jihar.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ke mayar da martani akan yajin aikin kungiyar ASUU da Jami’ar Sule Lamido reshen kafin Hausa ke yi a Jihar.
Gwamna Badaru ya ce ASUU a Jami’ar ta Sule Lamido mallakar gwamnati ba ta da hurumin ci gaba da yajin aikin.
Gwamnan ya bayyana cewa bai ga wani dalili da zai sanya jami’o’in Jihohi su ci gaba da gudanar da yajin aiki ba domin gwamnatin Jihar tuni da ta riga ta biya musu bukatun su.
Gwamna Muhammad Badaru ya kara da cewa ya kamata kungiyar ta yaba akan kokarin da gwamnatin ke yi.
Sannan Gwamna Badaru ya roki masu ruwa da tsaki da dattawa da ke Jihar da su sanya baki dangane da yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi don kawo karshensa.