Wani mamakon ruwan sama da aka tafka ya yi sanadin raba daruruwan mutanen kauyen Karnaya da ke Jihar Jigawa da muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa.

Ambaliyar ta kuma lalata fiye da rabin gidajen da ke kauyen.
Kauyen na Karnaya dai na dab da Dutse, babban birnin jihar jigawa.
Ambaliyar dai ta faru a sanadin maakon ruwan sama da aka fara tun misalin karfe 6:00 na yammacin Asabar ya tayar da mazauna kauyen tsaye har zuwa yammacin Lahadi, inda suka koma neman mafaka a azuzuwan makarantn yankin.
Daya daga cikin mazauna kauyen, Ado Karnaya, ya ce, tun jiya Lahadi har yanzu bai samu ya ci abinci ko kuma ya rintsa ba, Idonsu biyu suna kokarin tallafa wa ’yan uwansu.

Da aka tuntubi shugaban karamar hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), Yusuf Sani Babura, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce ambaliyar ta tashi kusan ilahirin garin, yayin da su kuma suke kokarin samar da matsugunai da abinci ga mutanen da lamarin ya shafa.