A kalla mutane shida ne suka suka rasa rayukansu bayan sun halarci wani biki a kauyen Akutara dake yankin Adani a karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Enugu a kwanakin karshen makon.
Rhotanni sun ce an kwantar da wasu a asibiti bayan halartar bikin gargajiya a Obollor-Eke dake karamar hukumar Udenu.
Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su mai suna Obinna Dike mai shekaru 31 kuma shi ne angon, wanda jama’a suka halarci bikinsa.
Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan Enugu, Daniel Ndukwe ya bayyana cewa Dike ya halarci bikin da ‘yan uwa da abokan arziki a ranar Juma’a.
Dukkansu sun koma gida Adani kuma suka cigaba da shagalin.
Wasegari babu wanda ya fito daga dakin da suka kwana, lamarin da yasa aka balle kofar inda aka samesu kwance kumfa na fita daga bakinsu.
Da gaggawa aka mika su asibiti inda aka tabbatar da mutuwar shida daga ciki kuma aka ajiye gawawwakinsu don binciken abinda ya kashe shi yayin da sauran ake kula da su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Enugu, Ahmed Ammani ya umarci sashen binciken manyan laifuka na CID da su kaddamar da bincike na musamman domin gano sarkakiyar dake tattare da lamarin.
A yayin ta’aziyya ga iyalan mamatan, kwamishinan ‘yan sandan yayi kira ga jama’a da su kwantar da hankansu tare da bada duk wani bayani mai muhimmanci ga ‘yan sanda yayin bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: