Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jajanta wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajanta wa al’ummar jihar Kano musamman wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya sanyawa hannu, Sarkin ya bayyana alhininsa game da ambaliyar ruwa da aka gani a wasu sassan jihar.

Sarkin ya yi kira ga al’uma da su guji zubar da shara a hanyoyin ruwa domin kaucewa afkuwar lamarin nan gaba.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya jaddada bukatar malamai su ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai domin magance matsalolin ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyyar rasa matsuguni da asarar dukiyoyi.