Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta sallami mutane huɗu bayan sun warke daga sabuwar annobar cutar ƙyandar biri a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Yakubu Nuhu  Danja ne ya sanar daka ranar Talata yayin ganawa da kwamitin kar ta kwana da masu ruwa da tsaki a kan cutar.

Ya ce gwamnatin ta samu rahoton mutane 27 da su ka kamu da cutar kum sun fito ne daga ƙananan hukumomi tara na jihar.

Sai da bayan mayar da hankali wajen ganin an basu kulawar da ta dace, daga bisani an gano huɗu daga ciki sun warke daga cutar.

Ya ƙara da cewa akwai wasu mutane 14 da ake jiran samakonsu zuwa yanzu, kuma ake sa ran sallamarsu idan aka tabbatar ba sa ɗauke da cutar a yanzu.

An samu ɓullar cutar ƙyandar biri a Najeriya, kuma ta ke ci gaba da yaɗuwa a sassa daban-daban na ƙasar har da babban birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: