Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Yobe YOSEMA ta bayyana cewa mamakon ruwan saman da aka tafka a Jihar a ranar Litinin yayi sanadiyyar Karyewar gadar Katarko da ke cikin karamar Hukumar Gujba ta Jihar.

Shugaban hukumar Dakta Muhammad Goje ne ya tabbatar da farwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Shugaban ya ce Gadar ta Katarko ta hada Jihohin Gombe Borno mai tazarar kilo mita 22 daga Damaturun ta jihar Yoben.

Dakta Muhammad ya ce Ambaliyar ruwan ta karya gadar baki dayan ta.

Shugaban ya kara da cewa sakamakon karyewar gadar ya haifar da nakasu mai girma ga ma’aikatan hukumar dangane da kokarin da hukumar ke yi wajen kai wa al’umma daukin gaggawa akan Ambaiyar ruwan da ta faru a kauyen Mutai da ke kusa da yankin wanda yayi sanadiyyar mamaye garin baki daya.
Shugaban ya ce Titin ya hada hanyoyi da dama da su ka hada da Damaturu babban Birnin Jihar zuwa Gujba Gulani da kuma kananan hukumomin Biu ta jihar Borno.
Dakta Muhammad Goje ya kara da cewa Ambaliya ta shafi garuruwan Gulani Buni Yadi Mutai wanda karyewar gadar ta Katarko zai haifar da tashin hankali ga mazauna garuruwan musamman kauyen Mutai.
Shugaban hukumar ya ce hakan ka iya shafar daukin da su ke kaiwa al’ummar yankunan.
Dakta Goje ya bayyana cewa kawo yanzu gwamnatin Jihar na nemo hanyoyin da za ta taimaka wadanda lamarin ya faru da su.