Hukumar hana cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta bayyana cewa za ta daukaka kara akan hukuncin da wata Kotu a Jihar ta yanke wa tsohon gwamnan Jihar Filato Janah Jang bisa tuhumar da hukumar ta ke yi da almundahanar naira biliyan 6.3.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanrwa da ta fitar a jiya juma’a,inda hukumar ta ce ta dauki matakin hakan ne bayan da Alkalin Kotun ya yanke hukuncin.
Hukumar ta ce hukuncin da kotun ta yanke ba ta gamsu da shi ba wanda hakan ne ya sanya za ta daukaka kara zuwa kotun gaba domin yin wata shari’ar.

Hukumar ta kara da cewa ta na zargin tsohon gwamnan da wani mai mai suna Yusuf Pam mai karbar kudi a Ofishin Sakataren gwamnan da yin sama da fadi da kudade da kuma.

Hukumar ta ce gwamnan yayi almubazzaranci da dukiyar Jihar ta Filato a yayin Mulkin sa.