Matashin da ya kashe mahaifansa a Jihar Jigawa mai suna Munkaila Ahmadu ya tabbatar da dalilan da ya sanya ya kashe mahaifan nasa da tabarya.

Munkaila ya bayyana cewa iyayen nasa su na kiransa da mahaukaci ne akan ya na yabon Manzon Allah S’A’W tare da kin yadda da wakokin yabon da ya ke yi.
Munkailan ya bayyana hakan ne ta cikin wani faifan bidiyo inda ya ce har yanzu bai yi nadamar kashe mahaifan nasa ba saboda ya yanke musu hukuncin wanda ya zagi Annabi Muhammad S,A,W ne.

Munkaila Ahmadu ya ce dukkan wanda ya zagi manzon Allah s,a,w hukuncin kisa ya tabbata a gareshi kuma babu gafara ga wanda ya aikata hakan.

Munkaila ya kara da cewa nan bada dadewa ba zai fitar da faifan bidyon sa wanda hakan zai iya sanyawa a sakeshi.
Kazalika Munkaila ya ce mahaifiyar sa ta na zuwa gidajen makota su na bayyana musu cewa shi mahaukaci ne saboda ba ya zuwa gona domin yin noma.