Gwamnatin tarayya ta gano wasu kadarori 14 wanda ake zargin Abba Kyari ya mallaka.

Tun tuni dai ake shari’a da babban jami’in ‘dan sandan wanda ake zargi da safarar kayan maye.

Binciken gwamnatin Najeriya ya gano akwai katafaren shaguna, rukunin gidaje da wani filin folo da Abba Kyari ya mallaka.

Haka zalika an gano wasu filaye da gidaje a hannun tsohon shugaban na dakarun IRT na kasa.

Rahoton yace DCP Kyari bai fadawa hukuma cewa yana da wadannan kadarori a babban birnin tarayya Abuja da garin Maiduguri a jihar Borno ba.

Baya ga haka, an samu fiye da Naira miliyan 207 da fam Є17,598 a wasu asusun bankinsa, darajar wadannan kudi na kasashen waje ya kai naira miliyan 10.

Wannan ya sa darakktan shari’a da gurfanarwa, J. Sunday ya shigar da karar Abba Kyari a kotu a madadin gwamnati, ana tuhumarsa da laifuffuka 24.

Ofishin Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin Najeriya yana zargin DCP Kyari da laifin boye gaskiya a game da mallakar wadannan dukiyoyi.

An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CR/408/22 a kotun tarayya ta garin Abuja.

Mohammed Kyari da Ali Kyari suna cikin wadanda ake tuhuma.

Baya ga shahararren ‘dan sandan da kuma ‘yanuwansa, gwamnati tana karar ACP Sunday Ubua wanda ya taba zama mataimakin DCP Abba Kyari a IRT.

Shi ma ACP Sunday Ubua ana tuhumarsa da aikata laifuffuka 24 a wata shari’ar daban a kotu.

Ana zargin Kyari ya mallaki gida a Blue Fountain Estate a Karsana da shago a Guzape, da wasu rukunin gidaje a Asokoro, duk a birnin Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: