Connect with us

Labarai

Mutunta Addinai A Kano Shi Ne Silar Zaman Lafiya – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya danganta zaman lafiya da ake samu a jihar da mutuntawa da hakuri da ake yi tsakanin kabilu da addinai a jihar.

Ganduje ya kuma ce duk wasu kabilu da kungiyoyin addinai a kasar nan yan uwan juna ne, don haka akwai bukatar su rungumi zaman lafiya da hadin kai ba tare da la’akari da banbancinsu ba don samun ci gaba da zaman lafiya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a karshen mako a Kano yayin da yake jawabi a fadar sarkin Yarbawa na jihar.

An dai gudanar da wani biki ne a fadar sarkin Yarbawar don murnar sarautar da aka baiwa gwamnan da matarsa a kwanakin baya a masarautar Ibadan.

A watan Yuni ne aka nadawa Ganduje da matarsa, Farfesa Hafsat Umar Ganduje sarautar Aare Fiwajoye da Yeye Aare Fiwajoye na kasar Ibadan.

Ganduje ya ce a shekarun baya, Kano ta yi fama da rikicin addinai da na kabilanci amma yanzu komai ya sauya saboda yadda ake nuna daidaito a tsakanin kabilu da addinai a jihar.

Ya kara da cewa dukkanin kabilu da ke zaune a jihar ana daukarsu ne a matsayin yan asalin jihar.

Sarkin Yarbawan Kano Injiniya Murtala Al’imash Otisese, ya ce bikin ya zama dole saboda sarautar ta dace da gwamnan da matarsa kuma ya cancanci karramawa.

Ya kuma bukaci gwamnan da bayar da fili don gina sakatariyar Yarbawa a jihar, wanda gwamnan ya yi alkawarin aikata hakan.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Mai Maganin Gargajiya Ya Harbi Kansa Bayan Yin Gajin Maganin Bindiga

Published

on

Wani mai maganin gargajiya mai suna Ismail Usman ya harbi kansa a lokacin da yake gwajin maganin bindiga a yankin Kuchibiyi da ke Karamar Hukumar Bwari a birnin Abuja.

Wani mazaunin Kuchibiyi Samson Ayuba ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, a lokacin da mutumin ya ke kokarin gada ingancin maganin bindgar da ya hada.

Ya ce sai dai bayan faruwar lamarin an yi gaggawar kai shi asibitin gwamnati da ke Kubwa bayan ya fadi, inda kuma ya samu raunuka.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin na Abuja Joesephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ta fitar.

Adeh ta ce sun samu rahotan cewa wani mai maganin gargajiya ya harbe kansa a lokacin da yake gwajin maganin bindigar da ya hada.

Sai dai ta ce sakamakon munanan raunukan da ya samu aka kai shi asibitin Kubwa domin duba lafiyarsa, daga bisani kuma aka mayar da shi asibitin kwararru da ke Gwagwalada domin kara samun kulawa.

Kakakin ta kara da cewa abinciken da aka gudanar a gidansa an gano wata bindigar gargajiya da layu wadanda ya yi amfani da su gurin gwajin maganin bindigar.

Adeh ta ce a halin yanzu su na ci gaba da gudanar da bincike kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar makami ba bisa ka’ida ba tare da yunkurin hallaka kansa.

 

Continue Reading

Labarai

Jami’an Soji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 100 A Sassan Najeriya A Mako Guda

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta ce jami’anta sun samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda 135, tare da kama mutane 185 da ake zargi da aikata laifuka, da kuma ceto mutane 129 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na fadin Kasar nan a cikin mako guda.

Daraktan yada yada labaran hedkwatar tsaro ta Kasa Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan ne a yau Asabar a hedkwatar da ke Abuja.

Buba ya ce daga cikin wadanda aka kama ciki harda 61 da ake zargi da satar mai.

Acewar Buba ‘yan ta’adda a yankin Arewa ta tsakiya sun fara mika wuya ga sojojin su.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Mayarwa Da Jami’ar Yusuf Maitama Sule Asalin Sunanta

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta mayarwa da Jami’ar Yusuf Maitama Sule tsohon sunanta na asali.

Majalisar Zartarwar jihar ce ta dauki matakin mayarwa da Jami’ar tsohon sunanta, bayan wani taro da gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a jiya Juma’a.

Idan ba a manta ba dai a watan Yulin shekarar 2017 ne tsohon gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya canjawa jami’ar suna zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule, domin tunawa da marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule, bisa irin gudummawar da ya bai’wa Jihar, dama Kasa baki daya.

 

Sai dai kuma a halin yanzu gwamnatin Jihar mai ci karkashin Jam’iyyar NNPP ta dauki matakin dawowa da Jami’ar tsohon sunanta.

Northwest University ya samo asali ne a zamanin mulkun tsohon gwamnan Jihar Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya samar da ita.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: