Mayakan Boko Haram da-dama sun rasa rayuwarsu yayin da wasu hare-hare da dakarun sojojin Najeriya suka kai masu a karshen makon jiya.

An hallaka ‘yan Boko Haram a hare-hare da sojoji suka kai masu a karshen makon.

‘Yan ta’addan sun mutu bayan luguden wuta daga jiragen sojojin sama da kuma rundunar sojojin kasa a wasu artabu da aka yi cikin ‘yan kwanakin nan.

Bayan luguden wuta da sojoji suka yi wa ‘yan ta’addan a Mantari, Mallum Masari da Gaizuwa, rundunar jami’an tsaro sun hallaka masu shirin jana’iza daga mayaƙan.

Rahoton yace a ranar Asabar, an hallaka wasu ragowar ‘yan ta’addan yayin da suka zo daukar gawar mayakansu da aka hallaka a Sheruri da Gabchari.

An samu gawawwakin ‘yan ta’addan na Boko Haram wadanda suka nutse a ruwa a Gabchari.

An kuma samu gawawwakin akalla mutane 9 da suka mutu a sakamakon harbin bindiga, daga ciki har da manyan jagorori Abou Zainab da Abou Idris.

Majiyar tace yayin da ‘yan ta’addan ke kokarin yi wa mamatansu sallar gawa, sai sojoji suka samu labari, nan da nan suka fara shawagi da sabon jirgin gaƙi na Super Tucano kuma su ka kashe wasu da dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: