Hukumar hana cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta gurfanar da kakakin majalisar dokokin jihar Ogun a gaban kotu.

Hukumar ta kama kakakin majalisar dokokin jihar ne a filin sauka da tashin jiragen sama na jihar Legas a makon da ya gabata.
An kama kakakin a bisa zargin karkatar da wasu kuɗade mallakin majalisar dokokin jihar Ogun da wasu zasge-zarge da ake yi a kansa.

Kuɗin da ake zargi ya yi sama da faɗi da su sun kai naira biliyan 2.5.

An gurfanar da Olakunle Oluomo a gaban babbar kotun tarayya da ke jihar Legas.
Rahotanni sun tabbatar da cewar hukumar ta gurfanar da akawun majalisar da daraktan kuɗi na majalisar dokokin jihar Ogun bisa zarginsu da hannu wajen karkatar da kudaɗe.
Mutanen uku ana girfanar da su bisa tuhuma 11 wanda su ka haɗa da bayar da bayanan ƙarya, satar kuɗi da kuma haɗa kai domin karkatar da kudaɗe.
Bayan karanta musu tuhumar a gaban kotu mutanen sun musanta zargin da ake yi a kansu.
Kafin kama kakakin majalisar, hukumar EFCC ta aike masa da takardar sammaci sau da dama sai dai bai amsa gayyatar hukumar ba ko sau ɗaya.