Kungiyar Malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU ta yi fatali da tayin da gwamnatin tarayya ta yi musu na karin kashi 35 cikin 100 ga furofesoshi da kashi 23.5 ga dukkan malamai da ma’aikatan jami’a na ƙasar.

Shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodoke ne yayi watsi da karin da gwamnatin ta yi musu.
Kungiyar ta ki amincewa da hakan ne bayan da gwamnatin ta bayyana musu iya abinda za ta iya karawa kungiyar kenan daga cikin abinda ta bukata.

Osodake ya bayyana cewa tayin da gwamnatin ta yi musu bashi da wani amfani sakamakon ba a kansa su ka yi yarjejeniya ba.

Shugaban ya kara da cewa tayin da gwamnatin ta yi musu ta yi hakan ne domin ta shafawa kungiyar kashin Kaji.
Farfesa Osodoke ya ce ya kamata gwamnatin ta cika musu yarjejeniyar da su ka cimma.
Sannan ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin karin da gwamnatin ta yi inda ya ce ta yi hakan ne domin batawa kungiyar suna.
Shugaban ya ce ba karin da gwamnatin ta yi musu su ke bukata ba so su ke a cimma yarjejeniya da aka ƙulla tsakaninsu.