Jami’an tsaron Kasar Masar sun kama mai shiga tsakanin gwamnatin Najeriya da ‘yan bindigan da su ka yi garkuwa da fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna zuwa Abuja tare da iyalinsa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami’an sun kama Tukur Mamu ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Kasar Saudiyya domin ibalar Umara inda aka tsare shi a tashar Jirgin AlKahira na kasar ta Masar na tsawon wuni guda.
A yayin hirar da aka yi dashi ya bayyana cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ce ta bayar da umarnin a kamashi.

Tukur Mamu ya ce bayan da jami’an tsaron su ka gudanar da bincike akansa ba su sameshi da komai ba.

Kazalika Mamu ya ce gwamnatin ta yi niyyar tsare shi ne kawai kamar yadda ta yiwa mai kokarin kafa Kasar Yarabawa Sunday Igboho, amma kuma hakan bai yuwu ba sakamakon dukkan takardun da ya tafi da su na gaskiya ne.
Ya kara da cewa bayan kammala binciken da jami’an tsaron su ka gudanar sun dawo da shi zuwa Najeriya.