Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta kama wani Umar Shehu da ake zargi da kai wa ƴan bindiga makamai a jihohin Neja, Kaduna da jihar Katsina.

An kama matashin mai shekaru 31 a duniya a Dikko Juncktion da ke ƙaramatr hukumar Gurara ta jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sndn jihar Wasiu Abiodun ya sanaywa hannu, ya ce wanda aka kama mai kimanin shekaru 31 ɗan asalin ƙaramar Funtua ne a jihar Katsina.

Matashin da aka kama ya na kai wa ƴan bindiga bindigu da harsaashi a dazukan Maidaro, Madaki a jihohin Kaduna da Katsina da kuma wasu snsanin ƴan bindiga a jihar Neja.

Sannan ƴan sanda sun kama wani Nasiru Musa wanda ke kaiwa ƴan binduga bayanai kuma ake zrginsa da hannu wajen kisan wasu mutane biyu a ƙaramar hukumar Tegina ta jihar Neja.
Ƴan sanda sun kama wasu mutane shida da ake zargi da kitsa kai hari ƙaramar hukumar Rafi, da Tegina a jihar.
Daga cikin waɗanda aka kama ya shaida cewar, su na gab da yin garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Rafi a jihar Neja.