Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bukaci shugabannin jami’o’in kasar da su nemi taimakon kungiyoyi da masu kudi domin karin samun kudaden shiga.

Ministan ilmi Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke kaddamar da majalisar gudanarwar jami’ar aikin Gona da ke Umdike Abeokuta Zuru da kuma Makurdi a jiya Alhamis.
Malam Adamu wanda ya samu wakilcin Goodluck Opiah ya bayyana cewa sakamakon halin da tattalin arzikin kasa ke ciki ne ya sanya gwamnatin ta ke neman hada gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu cikin fannin ilmi a manyan makarantu domin ta kara samun kudaden shiga.

Malam Adamu Adamu ya ce hakan ne ya sa su ke kira ga shugabannin jami’o’in da su nemo hanyoyin da za su dinga samun kudaden shiga.

Malam Adam ya kara da cewa ko da a gurin dai-daikun mutane ne masu tallafa wa da kuma kungiyoyi domin su kara akan na gwamnati domin su tsaya da kafafun su.
Ministan na ilmi ya ce yin hakan zai sa su samu girmama wa daga gurin mutune tare da bunkasa ilmin.
Malam Adamu ya bayyana cewa sharadin da aka sanya na sai shugaban jami’a ya fito daga yankin da ta ke ya haifar da rashin inganci ga ilmin Najeriya.
Inda ya ce ana duba cancantar mutum ne ba yankin da ya fito ba.