Jm’iyyar PDP ta tabbatar da cewa gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal bai sauka daga kan mukamin sa ba na shugaban gwamnonin jam’iyyar kamar yadda ake yadawa.

Babbanndarakta na kungiyar gwamnonin jam’iyyar ta PDP ne ya bayyana hakan a yayin wani jawabi da ya fitar.

Daraktan ya ce har kawo yanzu Tambuwal ya na nan akan mukamin sa kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda ya ke.

Darakta C.I.D Maduabum ya ce Aminu Waziri Tambuwal zai ci gaba da kokari wajen ganin ya shawo kan matsalolin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta a halin yanzu.

C.I.D ya bayyana wa masu ruwa da tsaki na cikin jam’iyyar da ma sauran mutane cewa har yanzu Tambuwal ya na nan akan kujerar sa.

Daraktan ya bayyana cewa Kungiyar PDP GF za ta shirya taro nan bada jimawa ba inda ta ke sa ran Tambuwal din ne zai jagoranci taron.

Ya ce wasu ne kawai a jiya Alhamis su ke yadawa cewa gwamna Aminu Waziri Tambwal ya sauka daga kan kujerarsa tare ayyana gwamnan Jihar Oyo amatsayin wanda ya maye gurbinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: