Hukumar kula da gudanarwar jami’ar Jihar Filato ta tabbata da cewa ba za ta sake bai wa malamin jami’ar da su ke yajin aiki albashi ba har sai sun koma sun ci gaba da ayyukansu.

Magatakardar Jami’ar Yakubu Ayuba shi ne ya bayyana hakan, ya ce matakin hakan na zuwa ne bayan wani taro da aka gudanar a garin Jos wanda majalisar gudanarwar jami’ar ta bayar da umarnin hakan.

Mista Yakubu ya bayyana cewa dalilan da su ka janyo kungiyar malaman jami’o’i ASUU da kungiyar Ma’aikatan jami’a SSANU su ka shiga yajin aiki duk an kawo karshen su.

Magatakardar ya kara da cewa tuni gwamnati ta sanya hannu akan takardar cimma matsaya da kungiyar ta ASUU kan bukatun ta guda takwas wanda ya haifar da yajin aikin.

Mista Yakubu Ayuba ya ce yajin aikin da malaman jami’ar Jihar ta Filato su ke yi kawai su na yi ne domin nuna goyan baya ga uwar kungiyar ta kasa ba don wani abu da ya shafe su ba.

Yakubu Ayuba ya tabbatar da cewa gwamnatin Jihar da hukumar gudanarwar jami’ar ne su ka dauki matakin kin biyan albashi ga dukkan ‘yan kungiyar ASUU da SSNU da ba su koma bakin aiki ba.

Ya bayyana cewa dukkan wanda ya dawo bakin aiki a fadin jami’ar za a rubuta sunansa a cikin rijistar sunaye domin cika umarnin da aka sanya.

A yayin jawabin shugaban kungiyar ta ASUU reshen Jihar Dakta Monday Hassan ya ce za su ci gaba da marawa uwar kungiyar su baya akan yajin aikin da ta ke yi.

Dakta Monday ya ce Jami’ar jihar ta ƙaru da ayyuka da dama daga kungiyar ta ASUU.

Leave a Reply

%d bloggers like this: