Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shigar da karar kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU akan kin janyewa daga yajin aikin da ta ke ciki.

Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi Chriss Ngige ne ya bayyana hakan.

Ngige ya ce gwamnatin ta dauki matakin hakan ne domin kungiyar ta yi gaggawar janye wa daga yajin aikin sai baba tagani da kungiyar ta shiga wanda aka ka sa cimma matsaya daga kowanne bangarorin guda biyu.

Ministan ya kara da cewa za a fara gudanar da shari’ar ne a gobe Litinin 12 ga watan Satumbar da mu ke ciki.

Ngige wanda ya aike da wata wasika ga babban magatakardar Kotun masana’antu ta Najeriya da ke birnin tarayya Abuja mai dauke da kwanan watan Takwas ga watan Satumba inda kuma kotun ta samu wasikar a ranar Tara ga watan.

Ministan ya bukaci kotun da ta yi gaggawar sauraran shari’ar domin ganin an kawo karshen yajin aiki.

Chriss Ngige ya bayyana cewa matakin hakan da ya dauka yayi daidai da damar da sashe na 17 na dokar takaddamar cinikayya ya bashi damar haka.

Gwamnatin ta shigar da karar kungiyar ta ASUU ne kwanaki kalilan bayan da gwamnatin tarayyar ta sanar da yiwa Kungiyar karin Albashi.

Baya ga karin albashin da gwamnatin ta yiwa kungiyar ta kuma yi musu alkawarin samar musu da naira biliyan 150 a lokacin da za a gudanar da kasafin shekarar 2023 mai zuwa wanda zai taimaka wajen farfado da jami’o’in gwamnatin Tarayya a fadin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: