Ma’aikatan filayen jiragen sama a Najeriya aun fata yajin aiki bayan umarnin uwar kungiyar ta sasa.

A Kano ma an rufe babban filin sauka daga tasoshin jiragen sama na Malam Aminu Kano a jihar.
Ma’aikatan sun dakatar da jigilar fasinja, tare da hana tasshin jirgin Azman zuwa Abuja da kuma jirgin Max Air zuwa jihar Legas.

Rahotanni daga filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano sun nuna cewar, bayan da fasinjoji su ka shiga jirgin ma’aikatan su ka hana tashin jirgin.

Yajin aikin da ƙungiyar ta fara ya biyo bayan wani saɓani da ƙumgiyar ta samu tsakaninta da hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya.
Ƙungiyar ta yanke shiga yajin aikin dagaa yau domin jan hankalin gwamnati don ganin an samar da daidaito tsakanin ma’aikatan da hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya.