Rundunar tsaron haɗin gwiwa sun samu nasarar dakile wani yunƙurin harin yan bindiga da su ka kai a jihar Katsina.

Yan bindiga sun yi ayari haye kan babura ɗauke da muggan makamai tare da nufin kai hari ƙaramar hukumar Batsari ta jihar.

Al’amarin ya faru a yammacin ranar Lahadi da kisalin karfe 04:30pm ba yamma.

Jami’an haɗin gwiwar da mafi yawansu mafarauta ne sun tinkari yan bindigan lamarin da ya kai ga su ka yi musayar wuta har su ka hallaka tara daga ciki.

Rahotanni sun tabbatar da cewar mafarautan sun kama wasu yan bindiga biyar daga cikin waɗanda su ka kai harin.

Wasu bayanai daga ciki nun nuna cewar akwai wasu mutane biyu da aka kashe daga cikin ƴan bindigan wanda adadinsu ya kai su 11.

Daga ɓangaren jami’an tsaro ba su ce komai a dangane da al’amarin ba, yayin da mai magana da yawun yan sandan jihar SP Gambo Isah ya ce bai samu cikakken bayani daga baturen yan sanda na yankin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: