Aƙalla ma’aikatan jinya 15,000 ne su ka fara yajin aiki a ƙasar Amuruka bisa ƙarancin albashi da rashin kulawa da walwalarsu.

Malaman jinyan da ke Minnesota da Wisconsin donnganin an kyauatata rayuwarsu.

Mai magana da yawun ƙungiyar malaman jinya na Minnesota ya ce za su shafe kwanaki uku su na yajin aikin wanda su ka fara ranar Litinin kuma za su ƙare ranar Alhamis da safe.

Da dama daga cikin malaman jinya sun yi dafifi a bakin wasu asibitocin da lamarin ya shafa.

Ma’aikatan lafiyan sun nuna damuwarsu matuƙa tun bayan ɓullar cutar Korona wanda aikin ya daɗa yi musu yawa ba tare da ƙarin albashi ba.

Kamar yadda su ka bayyana, akwai ƙarancin malaman jinya wanda hakan ya sa ayyuka su ka fi ƙarfinsu kuma babu ƙari a kan albashin da ake biyansu.

Wata ƙungiyar asibitoci ta shaida cewar sun shirya ƙarin albashi na kashi 10 zuwa 12 ga ma’aikatan, sai dai ma’aikatan na bukatar ƙarin albashi na kashi 27 zuwa 30 domin ci gaba da aiki yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: